Taimako game da kutsen asusu

Idan an yi wa asusunka kutse amma kana iya shiga asusun har yanzu, wannan shafin zai taimaka maka wajen kare asusunka, ya kuma dakatar da ayyukan da ba san da su ba. 

 

Shin an yi wa asusuna kutse?


Shin ko:

  • Ka ga post daga asusunka da baka yi tsammanin gani ba
  • Ka ga an tura Saƙonnin Kai tsaye da asusunka ba da izininka ba
  • Ka lura da wasu ayyukan asusu da ba kai ka aikata su, ko ka ba da damar a yi su ba (Kamar bi, ko daina-bi, ko toshewa)
  • Ka samu sanarwa daga gare mu da ta shaida maka cewa an yi wa asusunka kutse
  • Ka samu sanarwa daga gare mu da ta shaida maka cewa bayanin asusunka ya canza, alhali ba kai ka canza shi ba
  • Ka lura cewa kalmar sirrinka ta daina aiki kuma ana ba ka umarnin sake saita ta

 

Idan amsarka e ce ga ɗayan tambayoyin da ke sama, ɗan bi waɗannan matakan masu zuwa:


1. Canza kalmar sirrinka

Yi maza ka canza kalmar sirrinka a maɓallin shiga na Kalmar sirria cikin saituna. Idan an fitar da kai, to je ka Shiga sai ka danna Na Manta Kalmar sirri don sake saita kalmar sirrinka. Ɗan zaɓi kalmar sirri mai ƙarfi da ba a taɓa amfani da ita ba. 

2. Tabbatar cewa adireshin imel ɗinka yana da tsaro

Tabbatar cewa adireshin imel ɗin da aka haɗa da asusunka yana da tsaro kuma kai ne kawai ke da damar yin amfani da shi. Kana iya canza adireshin imel ɗinka ta manhajarka ta X (ta iOS ko Android) ko ta hanyar shiga cikin X.com da ziyartar maɓallin shiga na saitunan Asusu. Ziyarci wannan maƙalar don samun jagoranci game da sabunta adireshin imel ɗinka , duba wannan maƙalar kuma don samun ƙarin shawarwarin tsaro na asusun imel.

3. Soke haɗi ga manhajojin hulɗa na waje

Ziyarci Manhaja a cikin saituna, yayin da ka shige ciki. Soke damar shiga ga duk wata manhajar hulɗa ta waje da ba ka tantance ba.

4. Sabunta kalmar sirrinka a cikin amintattun manhajojin hulɗarka na waje

Idan amintacciyar manhajar waje tana amfani da kalmar sirrinka ta X, tabbatar ka sabunta kalmar sirrinka a manhajar. In ba haka ba, za a iya kulle asusunka na wucin gadi saboda gazawar yunƙure-yunƙuren shiga.

Yanzu kam asusunka zai samu aminci, kuma bai kamata ka sake ganin ayyukan asusun da ba ka yi tsammani ba daga yanzu. Idan har yanzu kana fuskantar matsaloli, ɗan tura neman tallafi don samun taimako.
 

5. Tuntuɓi Sashen Tallafi idan har yanzu kana buƙatar taimako

Idan har yanzu ka kasa shiga ciki bayan ka yi yunƙurin sake saita kalmar sirri, tuntube mu ta hanyar miƙa Neman Tallafi. Tabbatar ka yi amfani da adireshin imel ɗin da ka danganta da asusun X ɗin da aka yi wa kutse; daga nan sai mu aika da ƙarin bayani da umurnai zuwa ga wannan adireshin imel ɗin. Yayin da kake miƙa neman tallafi, ɗan haɗa da sunan mai amfani da kwanan watan ranar ƙarshe da ka samu damar shiga asusunka.


Ƙara koyo game da abin da za ka iya yi idan ka rasa damar yin amfani da asusun imel ɗin da ke haɗe da asusunka na X.

 

Kare asusunka ta ɗaukar matakan kariya masu sauƙi


Idan an yi wa asusunka kutse, bi waɗannan ƙarin matakan kariyar:

  • Share duk wani post da aka buga ba da son ranka ba lokacin da aka yi wa asusunka kutse.
  • Yi sikanin kwamfutarka don gano virus mabanbanta da manhajojin kutse musamman idan aka ci gaba da buga ayyukan asusu waɗanda ba a tantance ba bayan ka canza kalmar sirrin.
  • Girke cikon tsaro wa tsarin sarrafa na'urarka da manhajojinka.
  • Koyaushe yi amfani da sabuwar kalmar sirri mai ƙarfi, wadda ba ka amfani da ita a wani wurin, mai wuyar kintace.
  • Yi tunani game da yin amfani da tantancewa mai mataki biyu. Maimakon dogaro da kalmar sirri kawai, tantancewar shiga ciki na gabatar da matakin bincike na biyu don tabbatar da kai kaɗai ke da damar shiga asusunka na X.  Fasali ne na tsaro mai muhimmanci da ke ƙara matakin kariya ga asusunka, ya kuma rage haɗarin damar shigar da ba a tantance ba sosai.
  • Ƙin bayyana ma kowa bayanan shigarka hanya ce mai kyau ta tabbatar da rage haɗarin kutsen asusu.

Za ka iya samun ƙarin bayani a cikin shafinmu na shawarwarin kare asusu.

 

Ta yaya ake yi wa asusunka kutse? 


Za a iya yi wa asusunka kutse idan ka amince ma wata muguwar manhaja ko shafin yanar gizo da sunan amfaninka da kalmar sirrinka, ko idan kariyar asusun X ɗinka yayi rauni saboda rarraunar kalmar sirri, ko idan virus mabanbanta da manhajojin kutse da ke kan kwamfutarka masu kwasar kalmar sirri ne, ko kuma idan kana kan hanyar sadarwa wadda aka kutsa.

Ba koyaushe sabuntawar da ba a yi tsammani ba ke nuna cewa an yi wa asusunka kutse ba. Lokaci-lokaci, manhajojin hulɗa na waje kan iya samun tangarɗar da ke haifar da ayyukan da ba a yi tsammani ba. Idan ka ga wani baƙon aiki, canza kalmar sirrinka ko soke damar haɗi zai tsayar da shi, don manhajar za ta rasa damar shiga asusunka.

Zai fi kyau ka ɗauki mataki da wuri-wuri idan sabuntawa na bayyana a asusunka wadda ba ka buga ba, ko ka amince da ita ba. 

Yaɗa wannan maƙala